EFCC ta kama wani fasto bisa zargin damfarar Naira Biliyan 1.3

EFCC, kwato, naira, biliyan, Olukoyede
Shugaban hukumar EFCC ta Najeriya Mista Ola Olukoyede, ya ce a cikin kwana 100, ofishinsa ya samu ƙorafe-ƙorafe 5,000 da suka danganci almundahana, kuma ya...

Hukumar EFCC ta kama fasto Theophilus Oloche Ebonyi bisa zargin laifin damfarar kudi ga mambobin cocinsa da sauran ‘yan Najeriya ta hanyar amfani da tallafin bogi daga gidauniyar Ford har Naira Biliyan 1,319,040,274.31.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC Dele Oyewale ya fitar ranar Litinin.

Karanta wannan: Jihar Ribas: Kotu ta musanta bada belin magoya bayan Fubara

Sanarwar ta ce an kama Theophilus ne da laifin damfarar wadanda abin ya shafa, da suka hada da kungiyoyi masu zaman kansu NGOs da daidaikun mutane ta hanyar tallata wani shiri na shiga tsakani ta kungiyar sa ta (Theobarth Global Foundation), tana mai cewa gidauniyar Ford tana bayar da tallafin Dala Miliyan 20,000,000.000 don taimakawa kungiyar marasa karfi.

An ce Ebonyi yana sanarwa abokan huldarsa a wasu kafafen sada zumunta bayanan don tallata tallafin da ya samu daga gidauniyar Ford Foundation.

Karanta wannan: Masu zanga-zanga sun rufe hanyoyi a Minna

Sanarwar ta kara da cewa faston ya yaudari wadanda abin ya shafa da su yi rajista a matsayin wadanda suka ci gajiyar tallafin ta wayar tarho tare da neman su biya fom din rajista.

“Kowane mai biyan kuɗi an sanya shi ya biya Naira Dubu 1,800,000 ta hanyar wannan tsari.

“Binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa gidauniyar Ford ba ta da wani tsari ko tallafi ko dangantaka ko kuma wani kasuwanci da fasto din. Gidauniyar ta nuna rashin amincewa da shi da kungiyar sa, tare da jaddada cewa ba ta da alaka da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here