Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta Najeriya JAMB, ta fitar da sakamakon jarrabawar wadda ɗalibai suka sake rubutawa a cibiyoyin da aka samu tangarda yayin yin jarrabawar a bana.
A wata sanarwa da ya fitar da safiyar yau Lahadi, mai da yawun hukumar ta JAMB Dakta Fabian Benjamin, ya ce, sun kuma bankado yadda wasu ɗalibai suka aikata laifukan da suka saba doka yayin rubuta jarrabawar ta bana har ma da laifukan masu Cibiyoyin rubuta jarrabawar ta Kwamfuta watau CBT ke aikatawa, wadanda suka ta’azzara kura-kuran jarabawar.
Haka kuma ya ce, daga cikin dalibai 336,845 da a karshe aka shirya wa rubuta jarrabawar bayan samun daidaito a cibiyoyin da abin ya shafa an cire su, sannan aka kara da wadanda ba a tantance su a baya ba su kimanin ɗalibai 21,082 da ba su samu rubuta jarrabawar ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “ Idan za a iya tunawa, bayan kammala rubuta jarrabawar, an gudanar da taron shugabannin hukumar a dukkan jihohin tarayyar Najeriya domin duba sakamakon, wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban hukumar na kasa da sauran wasu manyan mana a fannin ilimi.
“Bayan an yi la’akari da rahoton jarabawar shiga jami’a, da kuma nazari mai zurfi a kansa, an kafa wani karamin kwamiti, karkashin jagorancin mataimakin shugaban jami’ar karatu daga gida Farfesa Olufemi Peters, don tabbatar da cewa sakamakon yana cikin tsari.













































