Tsohon Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar-Janar Abdulrahman Dambazau (Mai Ritaya), ya ce kafa ‘yan sandan jihohi zai iya yin tasiri a Najeriya ne kawai idan aka sanya shi a turbar kwararru sosai.
Dambazau ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a Abuja cewa dole ne a kebe ‘yan sandan jihohi daga ikon gwamnonin jihohi domin hana amfani da su wajen zaluntar abokan hamayya a siyasance.
Ya kuma yi kira da a tantance jami’an, tare da yin bincike da horo mai tsauri, marar sassauci don tabbatar da cancanta da hana rashin da’a.
Ya kara da cewa tsarin dole ne ya hada da kulawa da ka’idojin aiki na kasa baki daya don kare hakkin bil’adama ko na kabilanci.
“Saboda haka a takaice, ko da kana da ‘yan sanda na jihohi da na kasa, idan ba ka habaka inganci ba, ka sanya rundunar ta zama ta kwararru, ba za ka samu sakamakon da ake tsammani ba.”
Ya bayyana cewa dangane da rashin tsaro, al’ummomin da ake kai wa hari galibi na yankunan karkara ne, inda ya kara da cewa a wadancan wurare babu hukumomin tsaron da za su tabbatar da doka da oda.
“Watakila shi ne dalilin da ya sa mutane ke kira da a kafa ‘yan sandan jihohi. Amma ba shakka, ‘yan sandan jihohi suna bukatar abin da ‘yan sandan kasa ke bukata.
“Na yi imani mutane suna kira ga hakan ne saboda suna ganin tsarin da muke da shi ya yi gogara ne kan Tarayya, don haka idan ka raba shi, zai yi aiki. E, zai yi aiki ne kawai idan ka sanya shi ya zama na kwararru.
Dambazau ya kuma ce dole ne a kuma tabbatar sun cika mafi karancin ma’aunin ‘yan sanda na duniya, tare da tabbatar da cewa akwai amana.
“Kana gina amana da ƙarfin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da jama’a, ko na jihohi ne ko ba haka ba, domin inda jama’a ba su da amana, to matsala ce,” in ji shi.
Dambazau, wanda yanzu shi ne Ambasadan Najeriya mai a China, ya ce: “Shi ne dalilin da ya sa wani lokacin ma al’umma kan tara kudi su ba ‘yan bindiga domin su kare su daga wasu ‘yan bindiga.
“Saboda haka ni a wurina, ko ‘yan sandan jihohi ne ko ba haka ba, ma’aunin dole ne ya zama mai girma. Idan jihar ka kafa ‘yan sandan jihohi kuma ba a cika ma’aunin ba, to ka koma baya.
“Saboda haka ba shakka jihohin za su kasance a shirye su tallafa wa aikin yadda ya kamata, ci gaban dan adam abu ne mai mahimmanci wajen tabbatar da tsaro,” in ji shi.
(NAN)











































