Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai bar Abuja ranar Talata domin fara wata ziyarar ƙasa zuwa Birtaniya bisa gayyatar Sarkin Birtaniya sarki Charles III tare da matarsa sarauniya Camilla.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa bayanai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanar da hakan a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa shugaban ƙasar zai yi tafiyar tare da uwargidan shugaban ƙasa Oluremi Tinubu da wasu mambobin majalisar ministoci domin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu a fannoni kamar hijira, kasuwanci, zuba jari da musayar al’adu.
Bayo Onanuga ya bayyana cewa sarkin Birtaniya zai karɓi baƙuncin shugaban Najeriya da matarsa a Fadar Windsor daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Maris, inda za su duba wani baje kolin kayan tarihi daga tarin kayan sarauta na Royal Collection da suka shafi Najeriya.
Ziyarar ta zama ta farko da wani shugaban Najeriya zai kai cikin shekaru 37.
Haka kuma shugaban ƙasa Bola Tinubu shi ne shugaban Najeriya na farko da sarkin Birtaniya zai karɓa a Fadar Windsor.
A lokacin ziyarar, sarkin da shugaban ƙasar za su gudanar da tattaunawa ta sirri tare da ganawa da ƙungiyoyin da ke aiki a fannin tattaunawar addinai a matakin ƙasa da na duniya.
Haka kuma shugaban ƙasar zai halarci rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da kuɗi ta fam miliyan 746 tsakanin Hukumar Tallafin Fitar da Kaya ta Birtaniya UK Export Finance (UKEF) da Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya (NPA) tare da Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya domin tallafa wa gyaran manyan muhimman kayayyakin aikin ruwa na ƙasa guda biyu, wato tashar jiragen ruwa ta Lagos Port Complex da ke Apapa da kuma tashar jiragen ruwa ta Tin Can Island Port Complex.
Iyalan sarautar Birtaniya kuma za su shirya wani babban liyafar ƙasa domin girmama tawagar Najeriya.
A yayin ziyarar, shugaban ƙasa Bola Tinubu zai gana da Firaministan Birtaniya Keir Starmer a ofishin firaminista da ke 10 Downing Street, inda manyan jami’an ƙasashen biyu za su faɗaɗa haɗin gwiwa.
Ana sa ran ganawar za ta ƙare da rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da takardun fahimtar juna da dama da suka shafi kasuwanci, zuba jari, tsaro da haɗin gwiwar al’adu.
Daga cikin waɗanda za su raka shugaban ƙasar akwai shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a Lateef Fagbemi, ministan ma’adinai Dele Alake, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris, da karamar ministar harkokin waje Bianca Ojukwu tare da wasu manyan jami’an gwamnati.











































