Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta ce ya kamata babban bankin kasar, CBN ya yi la’akari da halin da masu karamin karfi da mazauna yankunan karkara suke idan aka daina karbar tsofaffin takardun kudi daga ranar 31 ga watan Janairu kamar yadda bankin ya tsara.
Kungiyar ta yi kiran ne yayin da gwamnonon jihohin Najeriyar ke ganawa da gwamnan babban bankin kan wannan batu.
Shugaban kungiyar ta NLC ya ce wajibi ne bankin ya sake nazari kan matakin domin kauce wa mawuyacin halin da mazauna yankunan karkara za su iya shiga da kuma asarar da za su tafka.
Kwamared Ayuba Waba shi ne shugaban kungiyar ta kwadago, ya shaida wa BBC cewa sun hango matsaloli a cikin shirin na Babban Bankin na Najeriya.
“Ina ganin kamar ba a yi hangen nesa ba. Kashi 70 na tattalin arzikinmu ya kunshi kananan ‘yan kasuwa ne.”
Ya ce mutum irin wannan na iya tafiya kasuwa da kazarsa ko akuyarsa ya sayar a irin wadannan kasuwannin na karkara. Idan ma babu kudi a hannu, “masu sana’ar POS za su iya biyansa kudi ba tare da sai ya tafi banki ba.”












































