Ƙungiyar ASUU na shirin tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya

asuu 1 1
asuu 1 1

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta fara ƙarfafa gwiwar membobinta a dukkan jami’o’in ƙasar domin shirye-shiryen fara yajin aiki na gargadi a matakin ƙasa.

Wannan mataki na zuwa ne mako guda kafin cikar wa’adin kwanaki 14 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya tun daga ranar 28 ga Satumba, 2025.

A cikin wata takarda da shugaban ƙungiyar, Farfesa Christopher Piwuna, ya sanya wa hannu a ranar 5 ga Oktoba, 2025, ASUU ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda gwamnati ke ci gaba da nuna shiru da sakaci wajen warware matsalolin da suka daɗe suna addabar tsarin jami’o’in ƙasar.

Ƙungiyar ta bayyana cewa a taron gaggawa da majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) ta gudanar a ranar 29 ga Satumba, ta nazarci sakamakon kuri’ar raba gardama da aka gudanar a sassan ƙungiyar, inda ta yanke shawarar bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 14 domin sanya hannu da kuma aiwatar da yarjejeniyar da aka sake tattaunawa tun watan Fabrairu, 2025.

Labari mai alaƙa: Yanzu-yanzu: ASUU ta yi barazanar fara yajin aiki, ta kuma bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14

Farfesa Piwuna ya nuna damuwa cewa duk da cewa ƙungiyar ta isar da matsayarta ga ministocin ƙwadago da ilimi, da kuma Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), gwamnati bata ɗauki wani mataki na zahiri ba har yanzu.

Ya bayyana cewa wannan mataki da ASUU ke ɗauka na nufin tilasta wa gwamnati ta cika alkawuranta, musamman ma batun sanya hannu da aiwatar da sabuwar yarjejeniyar, tare da magance sauran matsalolin da suka daɗe suna jawo cece-kuce.

Shugaban ASUU ya yaba da haƙuri da jajircewar membobinta tun farkon tattaunawar da ya ce ta ɗauki tsawon lokaci fiye da yadda ya kamata, yana mai kira gare su da su ƙara haɗin kai da faɗaɗa shirin yajin aikin a dukkan jami’o’i domin cimma manufar ƙungiyar.

ASUU ta kuma umarci membobinta da su riƙa karɓar umarni daga shugabannin rassan su da masu kula da yankuna, tare da halartar tarukan ƙungiya a kai a kai domin samun sabbin bayanai game da matakin da za a ɗauka nan gaba.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here