Zaben Fitar da Gwani: Ana ci gaba da kada kuria gadomin fitar da gwani tsakanin Yan takarar shugabancin kasa 14 na jam’iyyar APC

images 3 3 640x430 1
images 3 3 640x430 1

Tun cikin daren ranar Talata ne aka fara kada kuriar a Abuja babban burnin Najeriya domin fitar da wanda zai yi wa jam’iyyar APC takarar shugaban Kasa a zaben shekarar 2023.

Deligate  dubu 2 da 203 ne dai ke layin zaben domin fitar da guda cikin masu bukatar tsayawa takarar da suka hadar da Asiwaju Bola Tinubu, da mataimakin shugaban Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, da sauran Yan takara Mutum 9.

Har yanxu da muke hada wannan rahoto yan takara 14 ne ke neman sahalewar wadancan wakilan jamiyyar (wato Delegates).

Yan takarar sune Mista Chukwuemeka Nwajuba da Pastor Tunde Bakare, da Mista Ahmed Rufai, da Sanata l Rochas Okorocha, da Mista Jack Rich, sai Gwamna Ben Ayade, da Gwamna David Umuahi,da jagoran Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, da Sanata Ahmed Yarima, sai Dakta Ahmed Lawal, da Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo,da Mista Rotimi Amaechi, sai Gwamna Yahaya Bello da kuma Mista Ogbonnaya Onu.

Tun a baya dai 9 cikin yan takarar sun janye daga takarar da suka hadar da Uwargida Uju Kennedy-Ohnenye, da Dakta Felix Nicholas,sai tsohon Gwanna Godswill Akpabio, da tsohon Gwamna Ibikunle Amosun, da tsohon shugaban majalisar dattawa Dimeji Bankole sai Sanata Ajayi Boroffice da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar da Sanata Ken Nnamani da kuma Gwamna Kayode Fayemi.

Har kawo karfe 6:00 na Safiyar ranar Laraba 08 ga watan Yunin shekarar 2022 ana ci gaba da kada kuriar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here