Zaben 2023: ‘Yan takarkaru zasu sa hannu sau biyu akan takardar yarjejeniyar gudanar da yakin neman zabe ba tare da tashin hankali ba

images 15 2
images 15 2

Kwamatin tabbatar da zaman lafiya na kasa NPC, ya gayyaci jam’iyyu, ‘yan takarkarun shugabancin kasa tare da masu magana da yawun su, domin sa hannu kan takakar dar  yarjejeniyar gudanar da yakin neman zabe cikin lumana ba tare da tashin hankali ba, da kuma bayan sanar da sakamakon zabe.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN yaga takardar gayyatar, tayi nuni da cewa yan takarkaru tare da masu magana dayawun su zasu sa hannu akan takardar a ranar 29 ga watan Satumba na shekarar 2022, a dakin taro na kasa dake Abuja.

NAN ta rawaitu cewa takardar gayyatar na dauke da sa hannun shugaban kwamatin na NPC, Ganar Abdulsalami Abubakar mai ritaya.

“Sa hannu na farko za’a yishi ne a watan Satumba, sanan kuma za’a kara sa hannu a watan Junairu kafin zabe.”
“Manufar sa hannu farko shine jam’iyyu, yan takarkaru da masu magana da yawun su, su yi alkawari zasu gudanar da yake neman zaben su ba tare da tashin hankalin jama’a ba.” Inji wasikar.
“Manufar kwamatin shine samar da zaman lafiya yayi yakin neman zabe da kuma bayan an sanar da sakamakon zabe a kasa baki daya.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here