A ranar Alhamis ne rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama Adewumi Gabriel, shugaban ATM na bankin Access reshen Daura, bisa zargin hada baki da wani abokin aikinsa wajen sace zunzurutun kudi har Naira miliyan 18 daga asusun kwastomomi.
Adewumi ya amsa laifin hada baki da David Mesioye, wanda a yanzu haka, ta hanyar yin amfani da kwarewarsu na ayyukan bankin wajen aiwatar da satar da aka gano a yayin da ake tantancewa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Abubakar Aliyu, ya ce daga cikin kayayyakin baje kolin da aka kwato daga hannun Adewumi sun hada da Naira miliyan 10.18 daga asusun ajiyarsa na banki daban-daban da kuma tsabar kudi N366,900 da dai sauransu.