Tinubu zai kashe Tiriliyan biyar kan tallafin man fetur

Tinubu, tallafin, man, fetur
Bayan share tsawon lokaci ana takaddama kan batun janye tallafin man fetur a Najeriya, a karon farko cikin shekara guda gwamnatin tarayya ta sanar da sake...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Bayan share tsawon lokaci ana takaddama kan batun janye tallafin man fetur a Najeriya, a karon farko cikin shekara guda gwamnatin tarayya ta sanar da sake biyan tallafin man fetur din kasar ga al’umma.

Gwamnatin Najeriya ta sa kafa ta shure  tallafin man fetur din kasar a karon farko gwamnatin tarayya ta ce tana biyan tallafin man fetur yanzu haka, kana ministan kudin kasar Wale Edun ya ce Najeriyar na hasashen biyan Naira Triliyan 5.4 a matsayin kudaden tallafin man fetur din da al’ummar kasar suka amfana.

Karin labari: Gwamnatin Kano za ta sake inganta wuraren shakatawa da lambuna

A shekarar da tagabata gwamnatin Najeriya ta biya fiye da Naira Triliyan 3.6 da kasar ta biya a matsayin kudin tallafin mai bayan da ta sanar da cewa ta jefar da kwallon mangwaro ta huta da kuda.

Wannan lamari ya haifar da cece kuce a bakunan ‘yan Najeriya da dama musamman ma masana tattalin arziki da ‘yan siyasa.

Babban makasudin zare tallafin man fetur din tun a ranar farko ta karbar rantsuwar shugaban Najeriya Bola Tinubu na zaman hanya guda ta neman ceto tattalin arziki da mahukunta suka ce na kan hanyar rushewa.

Karin labari: “Kashi 70 cikin ɗari na yara a Najeriya ba su iya karatu da lissafi ba” – NIEPA

Zare tallafin man ya sa an fuskanci  tashin farashin man daga Naira 167 kan kowace lita kafin zartar da hukuncin zuwa Naira 800 a mafi yawan kasar a yanzu, hakan ya kara ruda ‘yan Najeriya da ke biyan hajar man a cikin tsada, amma kuma ake sanar da su cewa har yanzu ana ci gaba da biyan kudin tallafi daga aljihun gwamnati.

Gwamnatin Najeriya a yanzu na nuna alamun kasancewa cikin tsaka mai wuya bisa abatun na zare tallafin man fetur din, duba da karin farashin man da ya jefa kasar cikin sabon rikici wanda har yanzu gwamnatin Najeriya ke neman hanyoyin warware kullin zaren da ya sarke a tsakanta da ‘yan kwadago.

A yayin da a share guda kuma da ci gaba da biyan kudin tallafin na nufin kara shigar gwamnati a wani matsin rashin kudin da masu mulkin ke fatan amfani da su wajen ingantar raya kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here