Tinubu zai bar Abuja zuwa Saudiyya domin gudanar da Umara

Tinubu depart new

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Alhamis zuwa Makka, da ke Ƙasar Saudiyya, domin gudanar da Umara, ibadar Musulunci da ta ƙunshi ziyartar birni mai tsarki na Makka.

Wata sanarwa da Bayo Onanuga, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, ya fitar, ta ce ziyarar za ta bai wa shugaban ƙasar damar yin tunani, ibada da kuma addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa ga Najeriya.

“Yayin da yake Makka, Shugaba Tinubu zai gudanar da ibadun da suka shafi Umara, tare da neman shiriya da albarkar Allah ga Najeriya da al’ummarta.”

Kafin ya bar Abuja, Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da wasu kayan aiki da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta saya domin gudanar da ayyukanta, a ɓangaren da aka ware wa shugaban ƙasa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ana sa ran shugaban ƙasar zai dawo Najeriya a mako mai zuwa, bayan kammala ibadar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here