Sojojin Rasha sun fara kai farmaki a Ukraine

219F3FAF E387 4055 97DD 6F713F5C23A8
219F3FAF E387 4055 97DD 6F713F5C23A8

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kaddamar da wani farmaki na musamman na soji a yankin Donbas da ke gabashin Ukraine.

A wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin, ya bukaci sojojin Ukraine da ke fuskantar ‘yan tawaye da ke samun goyon bayan Rasha da su ajiye makamai su koma gidajensu.

Mista Putin ya ce Rasha ba ta shirya mamaye Ukraine ba, amma ya yi gargadin cewa martanin Moscow zai kasance “nan take” idan wani ya yi yunkurin kai wa Rasha hari.

A cikin wani sakon twitter, ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya rubuta cewa: “Biranen Ukraine masu zaman lafiya suna cikin tashin hankali. Wannan yakin zalunci ne. Ukraine za ta kare kanta kuma za ta yi nasara. Duniya gani kuma dole ne ta dakatar da Putin. Lokaci ya yi da za a dauki mataki yanzu.”

Rahotanni na nuna cewa yanzu haka  bama-bamai sun tashi a wasu garuruwan kasar ta Ukraine, da kuma harbe-harbe a kusa da babban filin jirgin saman Boryspil a babban birnin kasar Kyiv.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Washington da kawayenta za su mayar da martani cikin hadin kai da yanke hukunci kan “harin da sojojin Rasha suka kai ba gaira ba dalili” kan Ukraine.

“Shugaba Putin ya zabi yakin wanda zai kawo mummunar asarar rayuka da wahalhalun mutane,” in ji Mista Biden. “Duniya za ta dauki mataki kan Rasha.”

A wani yunƙuri na ƙarshe na hana yaƙi jim kaɗan kafin sanarwar Mista Putin, shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce Rasha za ta iya fara “babban yaƙi a Turai” kuma ya bukaci ‘yan ƙasar Rasha da su yi adawa da shi.

Mista Zelensky ya ce Rasha na da sojoji kusan 200,000 da dubban motocin yaki a kan iyakokin Ukraine.

Rasha ta fara yakin ne kwanaki kadan bayan amincewa da jamhuriyar jama’ar Donetsk da Luhansk da ke gabashin Ukraine. Yankunan da suka balle – wadanda ke iko da yankuna masu yawa na yankin Donbas – daga baya sun nemi Moscow ta ba da tallafin soji.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here