Sojoji sun cafke ƴan sandan boge biyu da tabar wiwi a Taraba

Fake Policemen

Sojojin brigade ta 6 tare da hadin gwiwar jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Taraba sun cafke wasu mutane biyu da suka sanya kayan kaki na ’yan sanda da ake zargi da safarar tabar wiwi a cikin manyan motoci biyu.

Wata sanarwa da Acting Mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojoji ta brigade ta 6, Laftanar Umar Muhammad, ya fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa an kama su ne a garin Wukari.

Ya ce bisa sahihan bayanan sirri da aka samu, sojoji tare da jami’an NDLEA sun tare motar a kan hanyar Takum da ke karamar hukumar Wukari, inda suka kama mutanen biyu da ke sanye Da Kayan ’yan sanda.

An gano cewa suna dauke da motoci biyu kirar Toyota Hilux da aka cika da abubuwan da ake zargin tabar wiwi ce.

Bincike ya tabbatar cewa babu ko daya daga cikinsu da yake aiki da rundunar ’yan sanda a halin yanzu.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa motar da aka kama ta biyu ta ƙunshe da manyan fakiti 1,134 na tabar wiwi da aka fito da su daga Akure a Jihar Ondo, ana nufin kai su Jihar Adamawa kafin a cafke su.

Karin labari: NDLEA ta kama wasu manyan dillalan miyagun ƙwayoyi su biyu ɗauke da tarin kwayoyi a Lagos

Duk da haka, wadanda ke cikin motar ta biyu sun tsere bayan ganin jami’an tsaro.

Sojoji sun mika mutanen biyu da aka kama tare da shaidun laifin ga ofishin NDLEA da ke Wukari domin ci gaba da bincike da gurfanarwa.

Kwamandan brigade ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba da hadin kai tsakanin sojoji da NDLEA, tare da jaddada kudirin rundunar na tabbatar da cewa Jihar Taraba ba za ta zama mafaka ga ’yan ta’adda ko masu laifi ba.

Ya bukaci jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai cikin lokaci domin karfafa ayyukan tsaro afadin jihar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here