Naira ta kara daraja a kasuwa

Naira Dollar

A ranar Larabar da ta gabata ne Naira ta kara daraja a kasuwannin Nigeria inda aka sayar da Naira 1,459.02 zuwa dala.

Bayanai daga dandalin ciniki na FMDQ sun nuna cewa Naira ta samu N61.38. Wannan ya nuna an samu kashi 4.04 cikin 100 idan aka kwatanta da ranar ciniki da ta gabata a ranar Talata, inda aka yi musayar kudin gida kan N1,520.40 zuwa dala.

A halin yanzu, a Investor’s da Exporter’s (I&E), Naira ta yi ciniki tsakanin N1,593 zuwa N1,401 akan dala. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here