Masu taimakawa Shugaba Buhari 4 Sun Kamu Da Corona.

President Buhari sad sad
President Buhari sad sad

Rahotanni dake fitowa daga fadar shugaban Kasa nacewa 4 daga masu taimakawa shugaban kasar sun kebe kawunan su sakamakon harbuwa da Corona.

Jaridar Solacebase akarshen mako, ta rawaito cikin wadanda lamarin harbuwar cutar ta shafa sun hada da sakataren dake kulada fadar shugaban Kasa, Tijjani Umar, da babban dogarin shugaban Kasar Yusuf Dodo, Se Aliyu Musa, babban jami’in tsaron sa, dakuma babban Mataimaki na musamman kan harkokin labarai Garba Shehu.

Rahotanni sun nuna cewa sakamakon gwajin cutar da akaiwa mutanen 4 yanuna cewa jami’an sun kamu da cutar, kamar yadda rahotonnin suka nuna Ministan labarai, Lai Muhammad shima ya kamu da cutar.

Sanarwar tace izuwa yanzu, Babu rahoton tsanantar cutar ga wadannan mutane sakamakon yi musu rigakafi kamar yadda aka umarta.

” E to gaskiya babu rahotannin tsanantar cutar saidai na dan yi zazzabi me samfurin cutar corona, ayanzu haka inajin dama dama biyon shan alluran rigakafi har guda uku” inji Garba Shehu

“Sannan ayanzu haka na kebe kaina kuma inashan magani da aka umarce ni, kuma za a sake gwada ni dan sake tabbatar dacewa banida kwayar cutar” Inji Garba Shehun

Ayanzu haka ana cigaba da gudanar da gwaje gwajen cutar ga dukkan ma’aikatan dake fadar shugaban kasar dan tabbatar da kawar da cutar

Idan za a Iya tunawa, Uwargidan shugaban Kasa, Aisha Buhari akwanakin baya, bayan dawowar ta daga birnin Istanbul ta umarci dukkanin ma’aikatan ofishinta dasu tafi hutu, tareda bada umarnin garkame ofishinta sai baba_ta_gani, Wanda Hakan bai rasa nasaba da kokarin kandagarkin yaduwar cutar corona.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here