Lai Mohammed ya sami sabon mukami a majalisar dinkin duniya

Lai Mohammed 300x200 1
Lai Mohammed 300x200 1

Tsohon ministan Buhari, Alhaji Lai Mohammed, ya sami sabon aiki a majalisar dinkin duniya, inda sakataren na majalisar kan harkokin yawon bude ido “United Nations World Tourism Organisation”  Mista Zurab Pololikashvili, ya nada shi a mastayin mai bashi shawara.

A cikin wata sanarwa da aka bawa kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN, ta nuna cewa an sanar da bawa Lai Mohammed mukamin ne a wajan wani taro da majalisar take gudanarwa a Mauritius.

Ya yin da yake karbar mukamin, Mohammed ya yi gudiya ga sakataren bisa bashi wannan mukami da akai, kuma ya yi alkawarin zage danste don ganin ya yi abinda ake tsamma ni daga gareshi.

“Naji dadin wannan mukami da mai girma Zurab Pololikashvili ya bani, kuma zan yi iya kokarina wajan gudanar da aikina yadda ya kamata.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here