Jami’ar FUTO ta maka ASUU a gaban kotu kan maganar bawa Pantami Farfesa

Minister of Communication and Digital Economy Dr. Isa Pantami
Minister of Communication and Digital Economy Dr. Isa Pantami

Shugabar jami’ar tarayya dake Owerri (FUTO), Farfesa Nnenna Oti, ta ce hukumar jami’ar ta garzaya kotu ne saboda kin amincewa da ASUU ta yi kan karin girma da ta jami’ar ta yi wa Dakta Isah Ibrahim Pantami zuwa matsayin Farfesa a fannin tsaro na Intanet.

Hakan ya biyo bayan barazanar da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi na kakabawa jami’ar FUTO takunkumi kan amincewa da Pantami a matsayin farfesa yayin da yake ci gaba da rike mukami a gwamnatin tarayya a matsayin minista.

Sai dai wani babban ma’aikacin gudanarwa a jami’ar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi ikirarin cewa ASUU ba ta da hurumin kutsawa cikin lamarin da ba ta da hurumin yi.

“Kamar yadda ASUU ba ta gaya wa majalisar jami’ar mutanen da zata bawa matsayin ba, don haka ASUU bai kamata tace taki amincewa ba. A doka, ba za ku iya janye abin da ba ku da shi. ASUU ba ta tsara nade-nade da karin girma. Wasu daga cikin wadannan abubuwan an samo su ne daga ka’idojin NUC, kuma kowace jami’a ta tsara matsayinta,” inji majiyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here