Indonesia ta yi barazanar dakatar da ayyyukan Facebook da Google da WhatsApp a Kasar

Indonesia to block Facebook Google WhatsApp new 1
Indonesia to block Facebook Google WhatsApp new 1

Hukumomi a Kasar Indonesiya sun shirya dakatar da aikace-aikacen kafofin sada zumunta da shafukan Internet wadanda suka hada da Google da Facebook,da WhatsApp a fadin kasar.

Hukumar kula da kafafen sadarwa da tattara bayanai ta kasar ce ta bayyana hakan a ranar Talata cewa za a toshe kafafen nan da kwanaki da kadan.

Tuni dai hukumar ta baiwa masu kamfanonin kafafen sadarwar zamanin dake kasar wa’adin zuwa ranar Laraba don kammala rajistar lasisi, idan ba haka ba, ma’aikatar za ta bayyana sunayensu cikin jerin wadanda ke gudanar da ayyukansu a kasar ba bisa ka’ida ba.

Yin rijistar wani bangare ne na sabuwar dokar kasar da ta fara gabatarwa tun a watan Janairun shekarar nan da muke ciki ta 2022, tana mai cewa duk kafafen fasahar zamani dole ne su tabbatar da yin lasisi don samun damar aiki.

Jaridar Solacebase ta Turanci ta cika shekaru biyar

Dokar dai ita ce za ta bawa hukumomin da abin ya shafa a kasar damar aiwatar da ayyukansu yadda yakamata don bawa kamfanonin damar cire duk wani abun da bai dace ba da wani ya dora a dandamalin ba bisa doka ba, cikin sa’o’i hudu kacal.

A halin yanzu gwamnatin Indonesiya na kokarin rage yada labaran karya, musamman gabanin babban zaben kasar a shekarar 2024.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here