Hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC, ta yi watsi da rahotannin cewa akwai jabun Fafesoshi a jami’o’in Najeriya.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da mukaddashin sakataren hukumar Chris Maiyaki ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Karanta wannan: Hukumar ‘yan sanda ta gargadi jami’anta da su guji karbar na goro a wajen masu neman aiki
Ya bayyana rahoton mai suna, “Kimanin farfesoshi 100 na bogi da aka bankado a jami’o’in Najeriya’, a matsayin hasashe na tunanin marubucin.
Maiyaki ya kuma bayyana wallafe-wallafen a matsayin rashin tunani da kuma makirci na wasu marasa kishin kasa don haifar da husuma da tashin hankali da kuma tada zaune tsaye a matakin kasa.
Karanta wannan: Muna samun ci gaba a yaki da miyagun laifuka-Gwamnatin Katsina
A cewarsa, dangane da bayanan da aka tabbatar, Hukumar ta fara buga jerin cikakkun Farfesoshi a shekarar 2019.
Ya kara da cewa za a yi nasara ne ta hanyar ci gaba da sabunta jerin sunayen kwararrun Farfesoshi.