Gwamna Bala ya naɗa mataimakan siyasa 168

Bala Mohammed 750x430

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya nada mataimakan harkokin siyasa 168 domin kara inganta harkokin gudanar da mulki da zurfafa jagoranci na hadin gwiwa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mukhtar Gidado, mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar ranar Talata a Bauchi.

Gidado ya ce matakin na daya daga cikin kokarin da gwamnan ke yi na ganin an kara hada kai, da inganta ayyukan yi, da samar da gwamnati mai nuna himmar cika muradun al’ummar jihar.

Ya ce nadin ya haɗa da manyan mataimaka na musamman, mataimaka na musamman da mataimaka na sirri.

Gidado ya ce nadin ya kunshi mataimaka 63, manyan mataimaka na musamman 60 da mataimaka na musamman 38, duk a kan harkokin siyasa da zamantakewa.

Karin karatu: Dalilina na sauya sheka zuwa SDP- El-Rufai

Sauran sun hada da manyan mataimaka na musamman guda biyar akan harkokin siyasa da al’umma, babban mataimaki na musamman kan al’amuran fensho, da kuma babban mataimaki na musamman kan al’amuran kwadago.

Ya ce, sabbin mataimakan da aka nada, wadanda akasari tsofaffin masu rike da mukaman siyasa ne a matakin kasa, jiha, da kananan hukumomi, an zabo su ne bisa cancant da gogewa har ma da kwarewar siyasa da iya shugabanci.

‘’Gwamnan ya bukace su da su karbi nadin nasu a matsayin wani kira zuwa ga babban aiki tare da jaddada bukatar sadaukar da kai, biyayya da tsarin tafiyar da al’umma.

Ya ce gwamnati na da yakinin cewa sabbin nade-naden da aka yi za su sa gwamnatin ta kara karfi kan nasarorin da ta samu, da gina gadon mulki na gaskiya, hada kai, da ci gaba mai dorewa. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here