Bayan yafiyar shugaban ƙasa, tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan ya ce “Allah ne ya yi amfani da Tinubu wajen nuna mini rahama”

WhatsApp Image 2025 10 09 at 20.41.22 750x430

Tsohon ɗan majalisar wakilai na tarayya, Farouk Muhammad Lawan, ya bayyana godiyarsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu bisa yadda ya sanya sunansa cikin waɗanda aka yafe wa ta hanyar izinin shugaban ƙasa.

Lawan ya bayyana wannan lamari a matsayin alamar rahamar Allah, yana mai cewa wannan yafi komai muhimmanci a rayuwarsa, domin ya nuna sabuwar dama da sake haɗuwa da kaddararsa.

Tsohon ɗan majalisar ya fitar da wannan sanarwa ne a jiya Alhamis, inda ya bayyana cewa wannan yafiya ta zama sabon farawa gare shi bayan shekaru biyar da ya shafe a gidan yari sakamakon hukuncin da kotun koli ta tabbatar masa a baya.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa Lawan, Faruk wanda ya taɓa zama shugaban kwamitin binciken tallafin man fetur a majalisar wakilai, an same shi da laifin karɓar cin hanci na dala miliyan uku daga wani attajiri a fannin man fetur.

Labari mai alaƙa: Tinubu ya yafe wa fursunoni 175 kamar yadda doka ta bashi dama

An tunatar da cewa kotun koli ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru biyar a kansa kafin daga baya aka sake shi daga gidan yari na Kuje a ranar 22 ga Oktoba, 2024, sakamakon nazarin ƙarar da ya shigar.

Lawan, wanda ya wakilci mazabar Bagwai da Shanono a jihar Kano, ya bayyana cewa duk tsawon lokacin da yake cikin jarrabawa bai taɓa rasa ban gaskiyarsa ga Allah da kuma ƙasar nan ba, yana mai cewa wannan kwarewa ta koya masa tawali’u da sake nazari kan rayuwa.

Ya kuma tabbatar da cewa yanzu hankalinsa ya dawo ga ci gaba da hidimar ƙasa, tare da sabunta alkawarin da yake da shi na taimakawa gina Najeriya.

Duk da haka, ya bayyana cewa bai yanke shawarar tsayawa takara ba a halin yanzu, sai dai yana nan cikin harkokin siyasa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here