Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayar da guraben karatu ga ɗalibai 1,000, inda kowanne ɗalibi zai samu tallafin da ya kai sama da naira dubu dari takwas (₦800,000).
An ƙaddamar da shirin a Jami’ar Bayero ta Kano a ranar Asabar, inda Barau, wanda Sanata Kawu Sumaila ya wakilta, ya bayyana cewa shirin na da nufin magance ƙalubalen kuɗin karatu da matasa ke fuskanta tare da ba su damar samun ilimi mai inganci.
Sanatan ya ce ilimi shi ne fifikonsa na farko, yana mai jaddada cewa wannan shiri na nuna jajircewarsa wajen gina makomar Najeriya ta hanyar ba matasa ilimi da ƙarfafa su.
Ya kuma ja hankalin waɗanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da damar yadda ya kamata, yana mai tunatar da su cewa wannan ba wai tallafin kuɗi kaɗai ba ne, illa dai kira ne zuwa ga hidima da kuma jajircewa wajen yin fice.
Karanta: Dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta dawo da darasin tarihi cikin kundin tsarin karatu – Minista
A gefe guda, Kawu ya ba kowane ɗalibi naira dubu ashirin (₦20,000) domin kuɗin sufuri.
Karamin ministan Gidaje da ci gaban Birane, Abdullahi Atah, ya yabawa wannan mataki, yana kiran shi abin koyi ga sauran ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki.
Haka zalika, Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana shirin a matsayin abin da ya zo a kan gaba kuma zai sauya al’amuran ɗalibai da dama.
Wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin, Fathiyya Musa da Hauwa Abubakar Ibrahim, sun nuna godiya tare da yin alƙawarin yin amfani da damar wajen inganta rayuwarsu.
Shirin ya yi daidai da manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya fi mai da hankali kan inganta ilimi, kiwon lafiya, tsaro, tattalin arziki da gine-gine.













































