Babu rahoton ɓullar cutar Ebola a Najeriya – NCDC

NCDC

Cibiyar daƙile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa (NCDC) ta fitar da sanarwar gargadi a fannin lafiya, bayan tabbatar da bullar sabuwar annobar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC). 

Sai dai cibiyar ta tabbatar da cewa babu rahoton ko guda da aka gano a Najeriya.

Ma’aikatar Lafiya ta Dimukradiyyar Congo ta bayyana cewa, zuwa ranar 4 ga Satumba, 2025, an samu mutane 28 da ake zargi da kamuwa da cutar da kuma mace-mace 15, ciki har da ma’aikatan lafiya hudu a lardin Kasai.

Gwajin dakin bincike a Kinshasa ya tabbatar da nau’in Ebola Zaire a matsayin sanadin barkewar cutar.

Karin karatu: Gwamnatin tarayya ta fayyace rawar da take takawa a fannin kiwon Lafiya a matakin farko

Duk da babu rahoton bullar cutar a Najeriya, NCDC ta ce an ƙara tsaurara matakan sa ido musamman a iyakoki da wuraren shiga ƙasa, tare da ƙarfafa cibiyoyin lafiya domin inganta hanyoyin kare kamuwa da cutar.

Hukumar ta yi gargadi cewa gano cutar da wuri, killace masu ita, da kuma ba su magani na tallafi na rage yawan mace-mace, ta kuma shawarci ‘yan Najeriya da su rika wanke hannu sosai, guje wa hulɗa da masu zazzaɓi, gudawa ko zubar jini ba tare da sanin dalili ba, da kuma nisantar daji da nama marar dahuwa.

An kuma ja hankalin ma’aikatan lafiya da su yi taka-tsantsan, su bi ka’idojin kare kansu daga kamuwa da cuta, kuma su rika bayar da rahoton duk wani zargi nan da nan.

An ce rigakafin cutar Ervebo yana nan a shirye ga nau’in Ebola Zaire, kuma ƙungiyoyin agaji tare da tallafin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun riga sun isa wuraren da cutar ta bulla a Dimukradiyyar Congo.

An shawarci matafiya da su guji tafiya zuwa ƙasashen da aka tabbatar da bullar Ebola, haka kuma, duk wanda ya shigo Najeriya daga irin waɗannan ƙasashe cikin kwanaki 21 kuma ya sami zazzaɓi, amai ko zubar jini ba tare da dalili ba, ya kira lambar gaggawa ta NCDC wato 6232 don a tantance shi.

Najeriya dai na ci gaba da fama da wasu annoba da suka haɗa da cutar Lassa, sankarau, diphtheria, masassara da anthrax.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here