Ana shirin fara yajin aiki a Kano bayan da NLC da TUC suka ki amincewa Ganduje ya mayar da tsohon tsarin albashi 

NLC rivers
NLC rivers

Kungiyar tuntuba ta hadin guiwa ta kungiyar ma’aikata a Kano za ta shiga yajin aiki, biyo bayan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na maido da tsohon tsarin albashi daga watan Fabrairu.

Bayan haka, kungiyoyin ma’aikatan sun yi watsi da tayin gwamnati na Naira 18,000 ga ma’aikatan kananan hukumomi da rage albashin ma’aikatan jihar.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis bayan taron gaggawa na kungiyar, shugaban kungiyar kwadago NLC a jihar Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir ya ce ma’aikata sun dauki matakin ne bayan da gwamnati ta ki amincewa da tayin maido da kudaden da aka cire daga albashi.

Kwamared Minjibir, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ta bakin shugaban ma’aikatan gwamnati Barr. Binta Lawal Ahmed ta shaida wa kungiyar ma’aikata cewa gwamnati ba za ta iya biyan mafi karancin albashi na N30,000 ga ma’aikata ba saboda gibin kasafin kudin da gwamnatin tarayya ta samu na watan Fabrairu.

A cewar Minjibir, shugabar ma’aikatan ta yi ikirarin cewa jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja sun raba Naira biliyan 544 na watan Fabrairu a kan Naira biliyan 699 da aka samu a watan da ya gabata, lamarin da ya yi illa ga gwamnatin jihar Kano wajen biyan kudaden da ake bin ta na wata-wata.

Shugabar ma’aikatan ta kira mu ta sanar da mu cewa akwai gibi a cikin rabon arzikin gwamnatin tarayya wanda ya sa ba za su iya biyan mafi karancin albashi ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here