Afcon: Cape Verde ta zama ƙasa ta farko da ta kai zagayen gaba

737d7740 b6f1 11ee 8f07 bbfdfa890097
737d7740 b6f1 11ee 8f07 bbfdfa890097

Cape Verde ta kasance ƙasa ta farko da ta kai zagayen gaba na ‘yan 16 bayan doke Mozambique da ci 3-0, a gasar kofin Afirka ta Afcon 2023 da ake gudanarwa a ƙasar Ivory Coast

Tsohon ɗan wasan Manchester United, wanda a yanzu ke taka leda a Rayo Vallecano, Bebe ne ya fara buɗe ragar Mozambique, bayan da ya ci ƙwallo mai ƙayatarwa a bugun tazara.

Daga nan Kaftin ɗin tawagar ƙasar, Ryan Mendes ya ƙara ta biyu.

Kafin daga bisani Kevin Pina ya ƙara ta uku daga wajen yadi na goma sha takwas.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here