Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jalingo ta kori Sanata Emmanuel Bwacha, Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu bisa zargin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, bayan ya lashe zaben sa a 2019 a karkashin jam’iyyar PDP.
Idan dai za a iya tunawa, jam’iyar PDP ta garzaya kotu domin neman hakkin jam’iyyarsu bayan da tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa ya koma APC a watan Fabrairu.
Mai shari’a Simon Amobeda wanda ya yanke hukunci kan lamarin cikin wata kara mai lamba, FHC/JAL/CS/9/2022 ya shaida wa Bwacha da ya gaggauta barin kujerar.
Amobeda ya yanke hukuncin cewa wanda ake kara na farko Emmanuel Bwacha, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a lokacin da aka zabe shi a zaben 2019.
Alkalin kotun da ya ambaci sashe na 68 (1) (g) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, ya ce wanda ya shigar da karar ya samu nasarar kafa hujjar sa, don haka yana da hakkin kan abin da ya nema.
Wani bangare na hukuncin ya kara da cewa “Ba tare da bata lokaci ba wanda ake kara na 3 (Hukumar zabe mai zaman kanta) za ta gudanar da zaben fidda gwani a tsakanin ‘yan takarar da suka fafata a zaben 2019 na mazabar Taraba ta Kudu a jihar Taraba.
“An umarci wanda ya shigar da kara da ya gabatar da wani dan takara don cike gurbin wanda ake kara na 1 cikin kwanaki 90 daga ranar da aka yanke wannan hukunci” inji hukuncin.












































