A wani bangare na bukukuwan sabuwar shekara, babban daraktan harkokin kasuwanci na hukumar gidaje ta tarayya Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya shirya addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da hadin kai a Najeriya da kuma samun nasarar takarar Bola Tunubu a zaben shugaban kasa a 2023.
Tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji na tarayya, ya kuma baiwa matasa 1,500 tallafin dogaro da kai, yayin da ya baiwa mata 1,500 tallafin karatu.
HOTUNA DAGA WAJEN TARON

A lokacin da yake jawabi ga manema labarai, a gidansa dake kauyen Kofa da ke karamar hukumar Bebeji a jihar Kano, ya ce ya kirawo malamai 2,500 domin yi wa kasar nan addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu addu’a dangane dq takarar shugaban kasa da zai yi a babban zabe na shekarar 2023 mai zuwa.
Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce yana goyon bayan Bola Ahmed Tinubu Saboda ya fi kowane dan takara cancanta yana mai cewa “Ni banga ga dalilin da zai sa Tunubu ba zai ci zabe ba domin shi mutum ne wanda ya san komai game da Najeriya, kuma bashi da kabilanci da zafin kai na addini, shi mutum ne wanda ya yadda da jam’iyya.
Da yake mayar da martani kan tambayar ko Bola Tunubu zai tsaya takara a zaben 2023 ko a’a, Kofa ya ce “Tuni aka warware wannan batun, ina mai tabbatar muku da cewa Bola Tunubu zai tsaya takara, yanzu haka ina magana daku a matsayin Darakta Janar na Tunubu Support Group Management Council, babbar cibiyar gudanarwa ta yakin neman zaben Tunubu.
Da yake magana kan sulhun da Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Kwankwaso, Abdulmumin Jibrin ya yi a kwanakin baya ya ce “Na yi imani da wannan sulhun, kuma zan ci gaba da ba da goyon baya don ganin an samu nasara, muna bukatar a ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa, don haka sulhun zai kawo sauyi mai kyau. .”












































