Ƙungiyar Malamai ta ƙasa ta bayyana damuwarta kan yaduwar wasu rahotanni na ƙarya da suka fito daga wasu kafafen watsa labarai na ƙasashen waje waɗanda ke ikirarin cewa an kashe dubban Kiristoci a Najeriya a bara.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Aminu Inuwa Muhammad, da sakataren ƙungiyar, Injiniya Basheer Adamu Aliyu, suka sanyawa hannu a ranar Alhamis, ƙungiyar ta ce waɗannan zarge-zargen ba su da tushe, rashin hankali ne kuma an tsara su ne domin ruɗar da al’ummar duniya tare da rura wutar ƙiyayya a Najeriya.
A cewar ƙungiyar, kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, ko da yake Najeriya na fuskantar ƙalubale na tsaro irin su ta’addanci, fashi da makami, da rikicin manoma da makiyaya, waɗannan duka laifuffuka ne da ke shafar Musulmi da Kiristoci baki ɗaya, ba wani yunkuri na kisan addini ba.
Ƙungiyar ta kuma yi Allah wadai da kafar Radio Genoa da wasu kafafen labarai na ƙasashen waje bisa yaɗa irin waɗannan bayanai marasa tushe.
Labari mai alaƙa: Gwamnatin tarayya ta karyata zargin kisan kiyashi ga Kiristoci
Ta ce wannan salon yada jita-jita yana iya haifar da tashin hankali da ɓarna, tare da ƙara rura wutar rikicin addini a ƙasar.
Ƙungiyar ta kuma tunatar da cewa addinin Musulunci ya haramta kisan duk wanda ba shi da laifi, inda ta ambaci ayar Alƙur’ani mai girma (Suratul Maidah, aya ta 32) wadda ke cewa: “Wanda ya kashe rai ba tare da hakki ba, tamkar ya kashe dukkan mutane ne; wanda kuma ya ceci rai, tamkar ya ceci dukkan mutane ne.”
A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga Musulmi da Kiristoci a Najeriya da su kasance ɗaya, su guji ruɗin ‘yan waje da ke ƙoƙarin kawo rikici a ƙasar.
Ta kuma yabawa jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu wajen yaki da ta’addanci, tare da roƙon gwamnati ta ƙara himma wajen dawo da zaman lafiya a sassan ƙasar.
Haka kuma, ta shawarci kafafen yada labarai na ƙasashen waje da su riƙa bayar da rahotanni masu gaskiya da adalci, tare da girmama bambancin al’ummar Najeriya, su guji yada bayanan da za su iya lalata zaman lafiya.












































