Zan mutu da tabon baƙin cikin sace ’yan matan Chibok -Jonathan

Goodluck Jonathan Okay ng 1 860x656 1 750x430

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa sace ’yan matan makarantar sakandaren Chibok a 2014 ya kasance babban tabo da ba zai gushe daga mulkinsa da rayuwarsa ba.

Jonathan ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin kaddamar da littafin da aka yiwa take da “Tabo: Tafiyar Najeriya da Rikicin Boko Haram” wanda tsohon hafsan hafsoshin tsaro, Lucky Irabor, ya rubuta.

Ya ce, “Wannan abu tabo ne da zan mutu da shi. Amma wata rana ana iya samun karin bayani, kuma hakan ya shafi Boko Haram.”

Ya kara da cewa a lokacin da gwamnatinsa ke kokarin tattaunawa da Boko Haram, kungiyar ta zabi Muhammadu Buhari a matsayin wakilinsu don jagorantar tattaunawa da gwamnati.

Jonathan ya bayyana cewa ya yi tsammanin lokacin da Buhari ya hau mulki a 2015, zai kasance hanya mai sauki wajen sasantawa da kungiyar, amma har yanzu matsalar Boko Haram tana ci gaba.

Karin labari: Atiku ya ƙaryata Labarin cewa zai janyewa wani takarar shugabanci

A cewarsa, wannan al’amari ya nuna cewa rikicin Boko Haram ya fi ƙarfin yadda ake dauka.

Tsohon shugaban ya kuma bayyana cewa Boko Haram ta fara ne tun 2009 lokacin da yake mataimakin shugaban kasa ga marigayi Umaru Musa Yar’Adua.

Bayan ya hau mulki a 2010, ya shafe shekaru biyar yana yaki da kungiyar har zuwa barinsa mulki a 2015.

Ya ce ya yi tsammanin Buhari zai iya kawar da kungiyar cikin lokaci, amma hakan bai samu ba har zuwa karshen rasuwarsa a watan Yuli 2025.

Jonathan ya kara da cewa rikicin Boko Haram ya fi fassarar yunwa ko matsalolin tattalin arziki kadai, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kafa kwamiti da dama tare da amfani da hanyoyi daban-daban wajen shawo kan lamarin.

Ya kuma yabawa Irabor saboda rubuta littafin, yana mai cewa ya dace duka sojojin da suka yi hulɗa da kungiyar su fitar da bayanai domin duniya ta fahimci hakikanin manufar Boko Haram.

Sai dai duk da tsawon lokaci da rikicin ya dauka, Jonathan ya nuna kwarin gwiwar cewa kasar za ta shawo kan Boko Haram a nan gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here