Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da wani sabon jadawalin sake komawa makarantun ta bayan kwashe watanni da rikicewar kalandar makarantu saboda munanan hare -haren ‘yan bindiga a jihar.
Kwamishinan ilimi na jihar, Shehu Makarfi, ya sanar da hakan a wajen wani taron bitar da Kungiyar Marubuta a fannin Ilimi ta Najeriya ta shirya.
Taron bitar, wanda aka shirya a matsayin wani ɓangare na bikin cika shekaru biyu na Ranar Kare Ilimi ta Duniya daga Hari, na da taken “Sakamakon hare -haren ta’addanci a kan Ilimi a Najeriya.”
Kwamishinan ya ce ana sa ran daliban jihar za su ci gaba da karatu a ranar Lahadi, 12 ga Satumba, 2021.
Saidai Ya ce, maimakon a ci gaba da karatu a zangon karatu na uku da aka soke a jihar, makarantun za su ci gaba da zangon farko na kalandar 2021/2022.
Karanta Wannan:Al’ajabi: Ana Zargin Wani Matashi Da Kashe Mahaifinsa A Jihar Kogi
Shehu Makarfi ya kara da cewa jihar ta fitar da dabaru don tabbatar da kammala wa’adin zango na uku ta hanyoyin yanar gizo.
Kwamishinan ya ce Zangon Farko zai fara daga 12 ga Satumba zuwa 17 ga Disamba; zango na Biyu, Janairu 9, 2022, zuwa 8 ga Afrilu, 2022; da zango na uku, Agusta 6, 2022, zuwa Satumba 3, 2022.
“Duk makarantun gwamnati da masu zaman kansu da na gaba da sakandare a cikin jihar dole ne su bi tsarin kalandar,” in ji shi.
Karanta Wannan:Majalisar Dokokin Jihar Legas Ta Kaddamar Da Dokar Karbar Harajin VAT, Dokar Hana Kiwo A Fili
Idan za a iya tunawa a baya an tsara cewa makarantun za su sake budewa a ranar 9 ga watan Agusta, domin zaman zangon karatu na uku na 2020/2021.
Duk da haka, gwamnatin jihar a ranar 6 ga watan Agusta, ta ɗage cigaba da aikin har zuwa wani lokaci saboda kalubalen tsaro.