‘Yan bindiga sun kai hari gidan Kwamishinan Shari’a na jihar Imo, tare da gidan mahaifinsa

Gunmen 2
Gunmen 2

Wasu ‘yan bindiga a cikin motoci kirar Toyota Hilux guda uku sun kai hari gidan kwamishinan shari’a na jihar Imo, Cyprian Akaolisa a ranar Lahadi.
Haka kuma an kone gidan mahaifinsa da ke Obibi ta Awo-Idemili cikin karamar hukumar Orsu ta jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa koda a shekarar daa ta gabata ma ta 2021 wasu ‘yan bindigar sun farmaki wani bangare na gidan kwamishinan.
Yayin harin na ranar Lahadi ‘yan bindigar sun lalata gidan kwamishinan da na mahaifinsa baki daya.
Kwamishinan ya tabbatar da harin a wata sanarwa da ya fitar a Owerri babban birnin jihar a ranar Lahadi, sai dai acikin sanarwar ya yi zargin cewa wadnda suka yi kone-konen ‘yan yankin Kudu maso Gabas ne.
“Igbo mutane ne masu aiki tukuru wadanda a cikin shekarun da suka kwashe suna kafa tsari ne tare da barin ci gaba a cikin al’ummominsu na asali.
“A cikin shekaru masu yawa na gwagwarmaya, na yi nasarar sanya wani shinge na gina wani gida da ya dace da iyalina; Mahaifina shima yana da gidansa da ya gina da guminsa.
“Amma a yau duka gine-ginen biyu sun lalace, sun zama toka sakamakon ’yan uwanmu Igbo sun kona su.
“Da farko dai, a shekarar da ta gabata, wadannan ‘yan bindiga sun kona gidana a Obibi cikin karamar hukumar Orsu ta jihar Imo, ba tare da wani dalili ba.
“A wannan shekarar kuma, sun kara dawowa sun kammala abinda suka fara a bara.
“A takaice dai, ina so in rubuta cewa gida na ya lalace gaba daya; sannan kuma sun yi amfani da babbar mota wajen kwashe dukkan kadarorin da muka mallaka a gidan ni da Iyali na.
“Mene ne laifina? Wa nayiwa laifi? Kuma menene laifin mahaifina”? Tambayoyin da Kwamishinan ya yi Kenan.
Har kawo lokacin da muke rubuta wannan Labari rundunar ‘Yan sandan jihar ba ta ce komai kan lamarin ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here