“Wasu Jami’ai a Gwamnati sun ci zarafina don naki sanya hannu kan lamunin dala miliyan 500” – Minista

Majalisar, Dokoki, Jami'ai, Gwamnati, zarafi, sanya, hannu, lamunin, dala, miliyan, Minista
Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta ce wasu jami'ai a gwamnati ne ke cin zarafinta saboda ta ki sanya hannu kan bukatar lamunin dala miliyan 500...

Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta ce wasu jami’ai a gwamnati ne ke cin zarafinta saboda ta ki sanya hannu kan bukatar lamunin dala miliyan 500 daga bankin duniya.

A ranar 10 ga watan Yuli, 2024, an dakile wata arangama ta zahiri tsakanin Kennedy-Ohanenye, da kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin mata da ci gaban jama’a a harabar majalisar dokoki ta kasa da ke Abuja, inda ministar ta bayyana cewa ta fayyace cece-kucen da aka yi mata kan Naira biliyan 1.5 da aka ware domin biyan ‘yan kwangilar da jami’an ma’aikatar suka yi.

Amma da ta ke zantawa da manema labarai ta wayar tarho, ministar ta ce “Akwai rancen dala miliyan 500 da na ke so na sa hannu, amma na ki sanya hannu. Haka kuma an samu dala miliyan 100 a baya ma.

Karin labari: KEDCO / NERC: Kungiyar DISCo ta bukaci sasantawa da kwastomomi

“Dukkan rancen da suke karba, gami da lamuni na Bankin Duniya, da sauransu, shin kuna sane da cewa ma’aikatar Bankin Duniya daya a Najeriya suna karbar kashi 40 cikin 100 kuma suna kiransa kudaden shawarwari?

“Waɗannan abubuwa ne da ya kamata ku yi la’akari da su. Jama’a ku maida hankali kan inda matsalar ta ke, ku bar ni ni kadai.”

Ta kara da cewa: “Yanzu, rayuwata na cikin hadari saboda na ki sanya hannu kan lamunin dala miliyan 500. Bari in gaya muku, idan na sanya hannu kan wannan lamuni a yau, ina da haƙƙin samun kashi biyar cikin ɗari na kuɗin, amma na ƙi sa hannu. Yana daga cikin dalilin da ya sa Majalisar Dokoki ta kasa da dukkansu suke bayana,” in ji Ohanenye.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here