Wadanda ke kokarin kore nasarorin da aka cimma a mulki na basa kyautawa-Buhari

IMG 20220914 WA0012
IMG 20220914 WA0012

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce duk da irin nasarori da kyakkyawar gwamnatinsa ta samu amma wadanda ya kamata su yi magana kan nasarorin da ya samu ba sa yin hakan.

Buhari, ya bayyana hakan ne ranar Talata a yayin wata liyafar karrama shi da aka gudanar a garin Owerri na jihar Imo lokacin ziyarar aiki ta kwana daya da ya kai jihar.

“La’akhari da lokaci da kuma albarkatu, wannan gwamnati ta yi kyakkyawan aiki.Dole ne in fada saboda wadanda ya kamata su fadi ba su fadi ba. Ban san dalili ba, ”in ji Buhari.

Shugaban ya zargi gwamnatocin da suka shude da gazawa wajen samar da ababen more rayuwa da bangaren wutar lantarki, duk kuwa da dimbin kudaden shigar da ake samu daga hako mai.

“A kan batun rashin tsaro da ‘yan fashin daji da gadar Neja ta biyu, idan ‘yan Nijeriya za su yi tunani; duk da haka, gaskiyar magana, ina zargin jiga-jigan Najeriya da rashin zama akan matsalolin da kuma yin tunani mai zurfi game da kasarmu,” inji Buhari.

“Tsakanin 1999 zuwa 2015 da muka shigo, zan so mutane su duba babban bankin kasa da kuma kamfanin mai na kasa NNPC. Matsakaicin abin da ake hakowa ya kai ganga miliyan 2 da dubu 100 a kowace rana kan farashin dala 100 kan kowace ganga.

Don haka Nijeriya tana samun riba a wannan lokaci ko wacce rana dala 100 sau yawan adadin ganga miliyan 2 da dubu 100 a wadannan shekarun.

Sai dai kuma, ana sukar gwamnatin Buhari da tabarbarewar basuka, da matsananciyar tabarbarewar tattalin arziki da kuma son zuciya wajen magance matsalar Fulani da makiyaya.

Bayanai daga ofishin kula da basuka na nuni da cewa adadin bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 41 a karkashin jagorancin Buhari.

A yayin da gwamnatin ke shirin ciyo bashin sama da Naira Tiriliyan 11 domin gudanar da kasafin kudin shekarar 2023, gwamnatin Buhari za ta bar wa Najeriya bashin Naira tiriliyan 50 idan ya bar mulki a watan Mayun shekara mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here