Hukumar gudanarwa ta jami’ar UNILORIN, ta amunce da nadin Dakta Kamaldeen Omo-Pupa, a matsayin mai kula da dakin karatu na jami’ar, da kuma Mr Ramoni Amaoo, a matsayin daraktan aiyuka na jami’ar.
Daraktan da ke kula da harkokin jami’ar, Mista Kunle Akogun, ne ya sanar da nadin nasu a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Ilorin.
Ya ce Omo-Pupa zai karbe aiki ne daga hannu Farfesa Abdulwahab Issa, wanda ya zangon shugabancin sa ya kare a watan Oktoba.
Akogun ya kara da cewa Omo-Pupa tsohon dalibin jami’ar Bayero ne, wanda ya sami digirinsa na farko a fanin kimiyar kula da dakin karatu a shekarar 1994.