Tinubu zai kai ziyara kasar Qatar don kasuwanci da zuba jari

Tinubu, kasar, Qatar, Najeriya, Legas, kasuwanci
A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu zai bar Najeriya zuwa kasar Qatar bisa gayyatar Sheikh Tamin Al-Thani sarkin Qatar. Kamar yadda Ajuri Ngelale, mai...

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu zai bar Najeriya zuwa kasar Qatar bisa gayyatar Sheikh Tamin Al-Thani sarkin Qatar.

Kamar yadda Ajuri Ngelale, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Ya ce Tinubu zai bar jihar Legas a ziyarar aiki na kwanaki biyu domin kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama da suka hada da tsaro da musanyar al’adu da bunkasar tattalin arziki.

A yayin ziyarar, ana sa ran shugaban kasar zai shaida rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da suka mayar da hankali wajen bunkasa fannin na Najeriya na hakika da kuma samar da jari mai amfani.

Karin labari: Kamfanin MTN ya bayyana dalilan katsewar sadarwa

Ngelale ya ce, yarjejeniyar za ta kasance ta fuskar kasuwanci da ilimi da al’adu tare da ma’adanai masu karfi hadi da tattalin arziki na dijital da kuma noma da mai da iskar gas tare da karfafa hadin gwiwa kan yaki da ta’addanci.

Ya kara da cewa, Tinubu zai kuma shiga wani taron kasuwanci da zuba jari tare da manyan jami’ai a sassa masu zaman kansu da na gwamnati na Najeriya da Qatar, don ciyar da damammaki daban-daban.

Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa manyan jami’an gwamnati ne zasu raka Tinubu domin rattaba hannu kan yarjeniyoyi kamar yadda NAN ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here