Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da kwamitin kidayar jama’a da gidaje na kasa da za a gudanar nan gaba.
Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahoton wucin gadi cikin makonni uku.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Tinubu shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Laraba.
Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, a wajen taron da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce kidayar na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa, da ingantaccen tsari, da kuma tsayar da shawara mai inganci a fannin kiwon lafiya, ilimi, tsaro, da tsare-tsare na tattalin arziki.
Ya kuma jaddada muhimmiyar rawa da za a yi kidayar ta hanyar fasaha wajen tabbatar da sahihin sakamako mai inganci da kuma bukatar yin hadin gwiwa tsakanin dukkan hukumomi da masu ruwa da tsaki.
Karin labarai: Kafofin sadarwar zamani yanzu sun zama ƙungiyar ta’addanci – Sultan
Ministan Kasafin Kudi da tsare tsaren tattalin arziki, Sanata Atiku Bagudu, wanda ke jagorantar kwamitin shugaban kasa kan kidayar jama’a da gidaje, ya tabbatar wa shugaban kasar cewa kwamitin zai gabatar da rahotonsa a cikin wa’adin makonni uku.
Yana mai cewa duk da kalubalen tattalin arzikin duniya, Najeriya na samun ci gaba a karkashin jagorancin shugaba Tinubu, inda ya yi nuni da cewa an samu kwanciyar hankali ta fuskar musayar kudaden waje da kuma kyakkyawan yanayin ci gaba.
Ya ce kwamitin zai ba da shawarar hanyoyin da za su dace, ciki har da dabarun tattara albarkatun cikin gida da na kasa da kasa don samar da kudaden kidayar.
A nasa bangaren, ministan yada labarai, Muhammed Idris, mamban kwamitin, ya jaddada cewa, sahihin bayanai na da matukar muhimmanci wajen tsarawa a dukkan bangarori, kuma kidayar jama’a ita ce ginshikin irin wadannan bayanai.
Shugaban hukumar kidaya ta kasa, Nasir Kwarra, wanda kuma zai zama sakataren kwamitin, ya ce tuni hukumar ta fara shirye-shiryen kidayar jama’a da gidaje na kasa tare da hadin gwiwar ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki da sauran masu ruwa da tsaki.
Kwarra ya bayyana cewa an mayar da hankali ne wajen gano muhimman abubuwan da ake bukata tare da aza harsashin da ya kamata shugaban kasa ya yanke shawara kan yadda ake gudanar da kidayar.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa hukumar kidaya ta kasa ta jajirce wajen ganin an gudanar da sahihin kididdigar ta hanyar fasaha da za ta taimaka wa tsare-tsare da ci gaban kasa.
Karin karatu: Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban rikon jihar Rivers
Kwamitin mai mambobi takwas ya hada da Ministan Kudi da tattalin Arziki, Shugaban Hukumar Kula da tattara Harajin Cikin Gida ta Tarayya, Darakta Janar na Hukumar Kula da Shaidar zama dan Kasa, Babban Sakataren Shugaban Kasa, da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Mulki da Ayyuka.
Kididdiga ta karshe a Najeriya ita ce a shekarar 2006, kusan shekaru ashirin da suka wuce.
Inda ta nuna yawan jama’a 140,431,790, tare da maza 71,345,488 da mata 69,086,302.