Kungiyar malaman makarantun kimiyya da fasaha ta kasa ASUP ta ce tabarbarewar ilimin da ake samu a yanzu yana da alaka da yadda gwamnati ke gazawa wajan samar da ci gaban makarantu.
Shugaban kungiyar ta kasa…Kwamared Anderson Ezbibe ne ya bayyana hakan a zagayen duba halin da makarantun kimiyya da fasaha su ke ciki a fadin kasar nan.
Ya ce ba lallai idan har gwmnati ba za ta rika girmama bukatunsu ba to wajibi ne su ma su rika tafiya yajin aiki kamar sauran kungiyoyin kasar na.
“Babban abun kunya ne yadda na ga makarantar kimiyya da fasaha ta garin Kano,wanda hakan ma nuna cewa gwamnatin jihar kano ba ta kula da makarantunmu”
“Akwai kaskanci kan yadda muka ga makarantar kimiyya da fasaha a jihar Kano”