T. Gwarzo – Hukuncin kotun Ƙolin Najeriya bai razana APC ba

T Gwarzo
T Gwarzo

Tun bayan yanke hukuncin ƙarshe da Kotun ƙolin Najeriya ta yi, wanda ya tabbatar da kujerun gwamnonin jihohin Kano da Zamfara da Filato da Bauchi, jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar nan ta ce hakan bai razana ta ba.

Jami’yyar ta ce akwai rata mai nisa tsakaninta da sauran jam’iyyun adawa kasancewar yawan jihohin da take da su, duk da ana ganin nasarorin da jam’iyyun adawar suka samu a kotun koli ta kara musu karfi.

Karanta wannan: Kano: Garin kwacen waya mota ta buge matashi ya mutu

A wata hirar da ya yi da BBC jigon jam’iyyar ta APC kuma, karamin ministan gidaje da raya birane Injiniya Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce duk wani gunagunin da ake yi lokaci ne zai tabbatar da asalin yadda lamura suke da kuma irin ƙarfin da jam’iyyar ta ke da shi a siyasan ce.

Ministan ya ce duk maganganun da ake ta yaɗawa game da jam’iyyar gabannin yanke hukuncin kotun duk labarai ne na ƙanzon-kurege, kuma asalin bayanai za su bayyana nan gaba. Ministan ya ƙara da cewa yanzu babu abinda jam’iyyar ke buƙata sai dai zaman lafiya da haɗin kai domin ta cimma manufofinta.

Karanta wannan: Majalisar dokokin Jihar Ribas za ta sa ke tantance tare da tabbatar da tsoffin Kwamishinoni 9

Ya yi bayanin cewa akwai dangantakar siyasa mai zurfi tsakanin ‘yan jami’iyyar APC da na sauran jam’iyyu kuma babu ta yadda siyasa ba ta kasancewa saboda haka dole ne mutane su kasance masu haƙuri da yanayin da suka sami kansu a fagen siyasa, kuma jam’iyyarsu ba ta fargabar duk wata haɗaka da ake raɗe-raɗin cewa jam’iyyun adawa na iya yi.

Gwarzo, ya kara bayyana cewa a yanzu haka dai suna duba na tsanaki tare da neman sanin ina da ina aka samu matsaloli domin a gyara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here