Sowore ya kai ƙarar DSS, Meta da X bisa zargin take masa haƙƙin ɗan adam

DSS Sowore Meta X logo Collage

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a zaɓen 2023, Omoyele Sowore, ya shigar da ƙarar take haƙƙin ɗan adam a kotun tarayya da ke Abuja, inda ya kai ƙara hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa (DSS), kamfanin Meta da kuma X, masu kula da manyan kafafen sada zumunta.

A cewar wata sanarwa daga tawagar lauyoyinsa a ranar Talata wacce Tope Temokun ya sanya wa hannu, ƙarar ta shafi abin da suka kira “ƙuntatawar da ba bisa doka ba” da aka yi wa asusun Sowore a dandalin Meta da X.

Lauyan ya ce batun yana da nasaba da kare ‘yancin faɗar albarkacin baki a Najeriya, yana mai jaddada cewa idan hukumomin tsaro za su riƙa umartar kafafen sadarwa a duniya kan wanda zai yi magana da abinda zai faɗa, to babu ɗan Najeriya da ya tsira daga murkushewa.

Lauyoyin Sowore sun yi nuni da cewa tsarin mulkin Najeriya, a sashen 39, ya bai wa kowane ɗan ƙasa cikakken ‘yancin bayyana ra’ayinsa ba tare da tsangwama ba. Sun ce haramtacciyar takunkumi kan sukar siyasa ba ta da alaƙa da dimokuraɗiyya, don haka duk wata hukuma ba ta da ikon dakatarwa ko gogewa.

Haka kuma, lauyoyin sun soki kamfanonin Meta da X kan amincewa da buƙatun da ba su da tushe, suna cewa hakan yana nuna goyon baya wajen hana jama’a yaƙi da danniya.

Labari mai alaƙa: Sowore ya kai ƙarar DSS, Meta da X bisa zargin take masa haƙƙin ɗan adam

Sun bayyana cewa wadannan kamfanoni ba za su iya ɓoye kansu da hujjar rashin tsoma baki ba yayin da ake juyar da dandalinsu zuwa wajen mulkin kama-karya.

Tawagar Sowore ta roƙi kotu da ta tabbatar da cewa DSS ba ta da ikon takaita ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta, tare da umartar Meta da X da kada su zama kayan aikin danniya. Sun yi kira ga ‘yan jarida, masu fafutuka da al’ummar Najeriya da su tsaya tsayin daka domin kare ‘yancin kowa daga irin wannan keta haƙƙi.

Ƙarar ta zo ne bayan DSS ta shigar da tuhuma mai ɗauke da ƙidaya guda biyar a kotun tarayya Abuja a kan Sowore, inda ta haɗa da Meta da X a matsayin wadanda ake ƙara.

Hakan ya faru ne bayan hukumar ta ba shi wa’adin mako guda daga ranar 8 ga Satumba da ya goge wasu rubuce-rubuce a shafinsa da suka shafi Shugaba Bola Tinubu, waɗanda DSS ta ce sun ƙunshi karya da tayar da fitina.

Wa’adin ya cika a ranar Litinin ba tare da ya goge rubutun ba, sannan kafafen sada zumunta suka ƙi amincewa da umarnin DSS na goge asusunsa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here