Shugaban kasar Kenya ya janye shirin haraji bayan gudanar da zanga-zanga

William, Ruto, Shugaban, kasar, Kenya, janye, shirin, haraji, zanga-zanga
Shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya ce zai janye kudirin dokar haraji da ke kunshe da cece-kuce a kan karin haraji bayan wata zanga-zangar da ta yi...

Shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya ce zai janye kudirin dokar haraji da ke kunshe da cece-kuce a kan karin haraji bayan wata zanga-zangar da ta yi sanadiyar kona majalisar a ranar Talata.

A wani jawabi da ya yi wa al’ummar kasar, ya ce ‘yan Kenya “ba sa son wani abu” game da kudirin.

“Na yarda,” in ji shi, ya kara da cewa ba zai sanya hannu kan kudirin dokar ba.

Karin labari: An kashe gobarar da ta tashi a matatar man fetur ta Dangote

Akalla mutane 22 ne aka kashe a zanga-zangar na ranar Talata, a cewar Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta Kenya (KNHRC).

A baya dai gwamnatin kasar ta yi korafin cewa ‘yan kasar Kenya na bukatar biyan karin haraji don rage basussukan da ake bin kasar na wani adadi mai yawa da ya haura dala biliyan 80 kwatankwacin fam biliyan 63, wanda ke kashe fiye da rabin kudaden harajin da kasar ke samu a duk shekara.

Karin labari: Yanzu-yanzu: El-Rufa’i ya maka majalisar dokokin jihar Kaduna a Kotu

Dokar ta asali ta gabatar da shawarar haraji kan burodi da man girki da sabis na hada-hadar kudi na wayar hannu da asibitoci na musamman da kuma kan ababan hawa wadanda ‘yan Kenya suka ce za su kara dagula matsalar tsadar rayuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here