Shugaba Tinubu ya sake sabbin nade-nade

Bola, Tinubu, shugaba, sake, sabbin, nade-nade
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin na tarayya guda takwas don cike guraben da ake da su a wasu jihohi da shiyyoyin siyasa a...

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin na tarayya guda takwas don cike guraben da ake da su a wasu jihohi da shiyyoyin siyasa a ma’aikatan gwamnati.

Cif Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce an nada sabbin sakatarorin dindindin ne bayan da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ya tantance.

Nade-naden sun hada da:

Karin labari: ‘Yan sanda sun kama mutane 2 da ake zargi da hannu wajan sace mahaifiyar Rarara

Dakta Emanso Umobong Okop na jihar Akwa-Ibom da Mista Obi Emeka Vitalis na jihar Anambra da Mahmood Fatima Sugra Tabi’a daga jihar Bauchi.

Haka zalika akwai, Danjuma Mohammed Sanusi na jihar Jigawa sai Olusanya Olubunmi na jihar Ondo da Dakta Keshinro Maryam Ismaila daga jihar Zamfara da kuma Akujobi Chinyere Ijeoma daga Kudu-maso-Gabas tare da Isokpunwu Christopher Osaruwanmwen.

“Shugaban kasa yana sa ran sabbin sakatarorin dindindin na tarayya za su nuna kwazo, da himma da rikon amana ga kasa wajen gudanar da ayyukansu tare da tabbatar da ingantacciyar hidima ga al’ummar Najeriya,” in ji sanarwar kamar yadda NAN ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here