Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa Dakar na kasar Senegal.
Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin cikar kasar Senegal shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Kasar Senegal na bikin ranar samun ‘yancin kai a ranar 4 ga watan Afrilun kowace shekara, inda ake bikin ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa a shekara ta 1960.
Ranar dai ta kasance cikin alfahari da al’ummar kasar, tare da shagulgula, fareti da al’adu.
Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce halartar Shettima taron an yi shi ne don girmama gayyatar da shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya yi wa shugaba Tinubu, biyo bayan kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriya da Senegal.
Za a gudanar da bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai a Place de la Nation da ke birnin Dakar, inda shugaba Faye zai karbi bakoncin mataimakin shugaban kasa Shettima da sauran manyan baki daga sassan Afirka da ma wajenta.
Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai dawo Najeriya bayan kammala taron na yini guda.