Sayar da filin Masallaci: Fitaccen malami ya yi murabus daga muƙaminsa

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi
Sheikh Tijjani Bala Kalarawi

Shahararren Malamin Addinin Musuluncin nan na jihar Kano Sheikh Tijjani Bala Ƙalarawi, ya yi murabus daga mukaminsa na kasancewa mamba a kwamitin amintattu na masallacin Juma’a na Abdullahi Bayero, da ke unguwar Fagge.

Sheikh Tijjani Ƙalarawi ya bayyana hakan ne yau Litinin, ta cikin shirin wani gidan rediyo a Kano wanda Solacebase ta bibiya.

Malamin ya ce, ya dace ya yi murabus daga zama memba na kwamitin amintattu saboda gine-gine marasa kima da rabe-raben filayen da ake yi daga cikin filin masallacin.

Haka kuma ya ƙara da cewa, yin hakan rashin kulawa ce ga wurin bautar ubangiji.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here