Sarkin Kano ya kai ziyarar ta’aziyya Ofishin jakadancin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a Abuja

IMG 20220520 WA0102 678x381 1
IMG 20220520 WA0102 678x381 1

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ya dawo Najeriya bayan kammala ziyarar da ya kai kasar Senegal a ranar Juma’a, ya ziyarci gidan gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE da ke Abuja, inda ya jajanta wa gwamnati da al’ummar masarautar bisa rasuwar shugaban ƙasar Sheikh Khalifa Bin Zayed Al Nahyan.

Solacebase ta ruwaito cewa, Bayan sarkin ya jajanta wa daular, ya kuma sanya hannu kan rajistar ta’aziyyar yana mai  cewa ƙasashen yankin Gulf da na yankin Gabas ta Tsakiya har ma da wasu ƙasashen da dama sun yi rashin wani babban shugaba da ya ba da gudummawarsa tare da sadaukar da kai wajen wanzar da zaman lafiya da harkokin tsaron ƙasa da ƙasa.

Ya ce, haƙiƙa Masarautar Kano ta yi alhinin wannan wannan babban rashi da zai yi wuyar cike gibinsa.

Haka kuma ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da sanya wa marigayi Sheikh Al-Nahyan ladan ayyukan alherin da ya bari.

Ya ƙara da cewa har abada za a ci gaba da tunawa da marigayi Shugaban ƙasar bisa karamcinsa da gudunmawar da ya bayar domin kare al’umma.

Mai Martaba ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin ya kuma sanya shi a Jannatil Firdausi.

Sarkin ya samu tarba daga Jakadan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a Najeriya Dakta Fahad Al Taffaq, inda ya gode masa bisa ziyarar da ya kai masa tare da yin addu’o’in fatan alheri.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here