Sarkin Kano ya bukaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayan abinci

Rikicin, Masarautar, Kano, Aminu, Ado, Bayero, umarci, Kotu, tarar, gwamnatin, Kano, naira, miliyan
Babbar kotu da ke zamanta a Kano ta umarci gwamnatin jihar ta biya Alhaji Aminu Ado Bayero diyyar Naira miliyan 10 saboda tauye hakkinsa...

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero ya yi kira ga ‘yan kasuwar kayayyakin masarufi da su rage tsadar kayan abinci da sauran kayayyaki domin baiwa talakawa damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki da yake karatowa.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Zaria yayin wata liyafa da aka shirya na wani littafi mai suna “Dauloli a Kasar Hausa” ma’ana ‘Masarautu a kasar Hausa’ na Farfesa Sa’idu-Mohammed Gusau.

Ado-Bayero ya kuma shawarci ’yan Najeriya masu hannu da shuni da su rika taimakawa marasa galihu a cikin watan Ramadan.

Karin labari: Daurawa ya sauka daga shugabancin hukumar Hisbah a Kano

Ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya kare rayukan al’umma su gudanar da azumin wannan wata mai alfarma cikin koshin lafiya tare da karban addu’o’i da sadaukarwa.

Sarkin ya yabawa mawallafin littafin, da ya yi bayani dalla-dalla kan masarautun Hausa a Kano da Katsina da Zamfara da Kebbi da kuma Zazzau da dai sauransu.

”Sun ba da cikakken bayani kan tsarin gudanar da mulki da kowace masarauta ta shimfida wadanda suka hada da sana’o’insu da ka’idoji da dabi’unsu,” inji shi.

Mawallafin littafin Farfesa Ahmed Zaria na Jami’ar Jihar Kaduna ya ce littafin mai shafuka 356 yana da babi 7.

Ahmed ya ce littafin ya ba da cikakken labari da tarihin masarautun Hausa da siyasarsu da tsarin mulki da ka’idoji da dabi’u tun daga kafuwarsa zuwa yau.

Karin labari: Kungiyoyin matasa a jihar Ogun sun bukaci Tinubu ya bude boda

Ya kara da cewa littafin ya zama kwafi ga dalibai da masu bincike a fannin ilimin harshe da tarihi.

Mawallafin, Farfesa Gusau ya ce littafin wani ƙoƙari ne na daidaita rubutaccen tarihin Masarautun Hausa inda ya ce galibin binciken da ake yi a jami’o’in na kan masarautu kaɗan ne ba duka ba.

Gusau ya kara da cewa littafin kuma wani yunkuri ne na tallafawa juna da karfafa hadin kai a tsakanin masarautun Hausa da sauran ‘yan Najeriya kamar yadda NAN ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here