Salihu Lukman ya magantu bayan ya yi murabus daga matsayin DG na kungiyar gwamnonin APC

2066E09F 7ECC 488D A804 1B7240C99E94
2066E09F 7ECC 488D A804 1B7240C99E94

Dr Salihu Lukman, Darakta-Janar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar  APC, ya tabbatar da murabus dinsa daga mukamin, yana mai cewa ya yi hakan ne domin kare mutuncin jam’iyyar APC.

Lukman, wanda aka yi rade-radin cewa ya mika takardar murabus dinsa a ranar Litinin, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba.

Ya ce ya yi murabus ne domin ya ci gaba da yakin neman dawo da jam’iyyar APC bisa manufar kafa ta, inda ya ce ficewar tasa ba za ta yi tasiri a yakin neman zabe ba.

“Shawarar da na yi na yin murabus daga mukamina shi ne don a ba ni damar ci gaba da fafutukar ganin an dawo da jam’iyyar APC bisa kudirin  da aka kafa ta, wato ta tsaya kan tsarin dimokuradiyya.

“Tun da labarin ya bayyana a ranar Litinin, 17 ga watan Janairu, game da murabus na a matsayin Darakta-Janar na PGF, da yawa daga shugabannin jam’iyyar, abokai, ‘yan uwa da masu fatan alheri sun isa gare ni da kalaman goyon baya da karfafa gwiwa.

“Mutane da yawa, musamman ‘yan jarida sun so a tabbatar da hakan. Zan iya tabbatar da cewa gaskiya ne; Na bayar takardar  murabus  ga shugaban dandalin, Gwamna Atiku Bagudu.

“Na kame kaina daga yin wata magana a bainar jama’a game da lamarin saboda har yanzu ina jiran amsa kan takardar ajiye mukamin dana mika,” in ji shi.

Ya yi nuni da cewa tun lokacin da zaben 2019 ke kara tabarbarewa, takaran cikin gida a jam’iyyar APC ta fara rugujewa yayin da wasu daga cikin shugabanninta suka nuna rashin hakuri.

Ya ce duk wani yunkuri na ganin shugabannin jam’iyyar su fara aiwatar da gyaran cikin gida an hana su.

Wannan a cewarsa, ya kasance musamman ganin yadda wasu jiga-jigan jam’iyyar a yunkurinsu na fitowa takarar mukamai suka zama masu gaba a yayin da yakin neman zaben jam’iyyar ya koma kusan yanayin yaki a lokuta da dama.

Ya kara da cewa duk da jam’iyyar ta sanar da ranar 26 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a gudanar da babban taron, amma yana da kyau shugabannin da jam’iyyar zata zaba su kasance zasu iya jure duk wani kalubale da zasu fuskanta

“Aiki na gaba da ke gaban dukkan shugabannin jam’iyyar shi ne tabbatar da sabbin shugabannin jam’iyyar da za su fito daga babban taron kasa za su kasance masu juriya da tabbatar dimokuradiyya da kuma yun kokari wajen samar da shugabanci na gari.” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here