NSCDC da hukumar kula da shige da fice da ta gidan yari za su ɗauki ma’aikata

NSCDC new

Hukumar kula da hukumomin tsaro na Civil Defence da ta kula da gidajen gyaran hali da kuma hukumar kula da shige da fice ta CDCFIB, ta bukaci wadanda suka cancanta da su nemi aiki a hukumomin daga ranar Alhamis.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da sakataren hukumar Manjo Janar Abdulmalik Jubril, ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Ya bukaci masu neman aiki da ke da sha’awar shiga aikin Hukumar tsaro ta Civil Defence NSCDC da Hukumar Kula da gidajen Gyaran hali da hukumar kula da shige da fice da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da su yi amfani da shafin Internet na hukumar wajen neman aikin.

“Ya kamata a gabatar da aikace-aikacen bisa tsari a cikin makonni uku daga ranar da aka fitar da wannan sanarwa, kuma ku lura cewa cikewar kyauta ne,” in ji shi.

Ya kuma jaddada cewa dole ne masu neman kowane daya daga coikin wadannan ayyuka a hukumomi huɗu da suke so, saboda aikace-aikacen da su bi ka’idoji.

Ya kara da cewa akwai guraben aiki na mukaman Sifurtanda da Sufeta da sauransu.

Sakataren ya ci gaba da cewa, ga matsayin Sifeto CONHESS 06, masu neman aikin dole ne su kasance masu rijistar ma’aikatan jinya ko ungozoma, inda ya kara da cewa matsayin na NCoS da NSCDC da FFS ne kawai.

Ga Mataimakin Sifeto kuwa CONPASS 06, masu nema dole ne su kasance masu shaidar kammala Diploma ko NCE a kowane fanni mai alaƙa da aikin.

Jubril ya ci gaba da cewa, abubuwan da suka wajaba don daukar ma’aikata sun hada da kasancewar mutum dan Najeriya sai cancanta da lafiyar kana su kasance ba su da wani hukunci ko bayanan zamba wadanda kuma ba su ke tsakanin shekaru 18 zuwa 35 da.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here