Nollywood ta shirya fina finai 635 cikin watanni 3

Nollywood
Nollywood

Hukumar kididdiga ta kasa NBC, ta ce adadin fina finan da masana’antar shirya fina finai ta Nollywood ta shirya a rubu’i na biyu na bana, ya karu zuwa 635, daga 416 da ya kasance a rubu’in farko na bana.

Hukumar ta wallafa adadin ne ranar Laraba a shafinta na website, cikin rahoton alkaluman fina-finan da Nollywood ta shirya a rubu’i na biyu na bana.

Bisa rahoton, adadin fina finan na rubu’i na biyu na bana, ya nuna an samu karuwar kaso 53.93 kan na rubu’in farko da kuma kaso 1.44 kan na shekarar da ta gabata.

Cikin nazarin da ya shafi wurare, hukumar ta ce jihar Lagos ce ke da adadi mafi yawa na fina finan da aka shirya da yawansu ya kai 234, sai Abuja dake bi mata baya da fina finai 196, sai Onitsha mai fina finai 174.

Banda wadannan, Jos na da fina finai 9, Kano na da 6, yayin da Benin da Fatakwal ke da akalla 7 kowannensu.

Hukumar NBS ta ce ta tabbatar tare da tantance adadin ne daga wanda hukumar tace fina finai ta kasa ta samar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here