Naira ta ragu zuwa 1,500 a kasuwar canjin kudade

naira, Dollar, ragu, kasuwa, canjin, kudade
A ranar Larabar da ta gabata ne darajar Naira ta ragu zuwa 1,500 a kasuwar hada-hadar canjin kudade. Farashin ya ragu da kashi 3.45 daga Naira 1,450 kan...

A ranar Larabar da ta gabata ne darajar Naira ta ragu zuwa 1,500 a kasuwar hada-hadar canjin kudade.

Farashin ya ragu da kashi 3.45 daga Naira 1,450 kan kowacce Dala da aka samu a ranar Litinin.

Dillalan kudi a Legas wanda kuma aka fi sani da BDC, sun bayyana farashin siyan kore a kan Naira 1,490 da kuma farashin sayar da su kan Naira 1,500 inda ka samu ribar Naira 10.

Karanta wannan: Ministocin wajen kasashen ECOWAS na taro a Abuja kan rikicin siyasar yankin

Nairar dai ta kara daraja da kashi 1.05 zuwa Naira 1,418/$ a ranar Laraba daga Naira 1,433/$ a ranar Talata.

A cewar FMDQ Exchange, wani dandali dake sa ido kan kasuwancin musanya na kasashen waje a Najeriya, Naira ta kai Naira 1,510 kuma ta kai Naira 896.28 inda ake samun cinikin Dala Miliyan 203.93 a kullum.

Karanta wannan: Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyya ga iyalan Ojougboh

A halin da ake ciki a ranar 1 ga watan Fabrairu 2024 CBN, ya ci gaba da sauye-sauyen da yake yi a kasuwar canji ta hanyar cire kayyade farashin FX da masu hada-hadar kudi na duniya IMTOs suka yi.

“Don kaucewa shakku, an cire iyakar -2.5% zuwa + 2.5% a kusa da ranar da ta gabata ta rufe kasuwar musayar kudaden waje ta Najeriya,” a cewar babban bankin CBN.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here