Naira ta kara daraja a kasuwar canjin kudade

Naira, Dala, daraja, kasuwa, canjin, kudade
Naira a ranar Litinin ta kara daraja a kasuwar canji inda aka sayar da ita kan Naira 1,354.21 zuwa Dala. Bayanai daga dandalin ciniki na FMDQ, wani dandali...

Naira a ranar Litinin ta kara daraja a kasuwar canji inda aka sayar da ita kan Naira 1,354.21 zuwa Dala.

Bayanai daga dandalin ciniki na FMDQ, wani dandali ne da ke kula da kasuwar musayar kudaden waje ta Najeriya (NAFEM), ya nuna cewa Naira ta karu da kashi N46.19.

Wannan ya nuna an samu kashi 3.29 cikin 100 idan aka kwatanta da cinikin baya a ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu, inda aka canza ta a kan Naira 1,400.40 zuwa Dala.

Karin labari: Rundunar sojin saman Najeriya ta bada umarnin binciken mutuwar Yusuf Shu’aibu

Koyaya, jimlar cinikin yau da kullum ya ragu zuwa dala miliyan 84.83 a ranar Litinin, ya ragu daga dala miliyan 201.88 da aka samu a ranar Juma’a.

A halin da ake ciki, a tagar Investor’s da Exporter’s (I&E), Naira ta yi ciniki tsakanin N1,441.00 zuwa N1,285.00 akan Dala.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here